Hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce tashin hankali mai nasaba da ayyukan ƴan bindiga ya tilasta wa mutum sama da dubu 16 barin muhallanssu a tafkin Tchadi daga watan Janairu zuwa Maris shekara 2026.
A rahoton da ta fitar, ta ce duk da an samu ragowar ayyukan ƴan bindiga idan aka ƙwatanta da shekara bara ƴan bindigar sun kashe mutum 22 sannan sun jikkata wasu 36 yayin da su ka yi awon gaba da mutum 109 a hare-hare 63 da suka kai a watanni ukun farko na wannan shekara.
Yankunan da lamarin yafi kamari sun hada da Wadi Hawar da Wadi Fira da Tama da Kobe sai kuma yankin Ouaddai da ke gabashin ƙasar.
Rahotanni su ce a yayin da damuna ta fara kankama sannan yanayin tsaro ke kara ta’azzara yan gudun hijra na cigaba da kwarara zuwa yankunan abin da ke barazanar haifar da karancin abinci da ababen more rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login