Labarai
kotun ta yanke wa jagororin kungiyar ta’addanci ta Ansaru hukuncin daurin rai da rai

Shugabannin Ansaru da gwamnatin Najeriya ke zargi da laifukan ta’addanci sun sun amsa laifukansu a kotu, bayan shafe watanni suna musanta zarge-zargen.
An kama mutanen ne tun a shekarar 2025 bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai musu.
Mutanen biyu da ake zargi Mahmud Usman, wanda hukumomi suka ce shi ne jagoran ƙungiyar Ansaru, da kuma Abubakar Abba, wanda ake zargi dan shi ne mataimakinsa sun amsa dukkan tuhume-tuhumen 32 da ake musu.
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyansu Bala Dakum ya shaida wa kotun cewa bayan tattaunawa da waɗanda ya ke karewa, sun amince da tuhume-tuhumen bayan sake karanta mu su a gaban kotun.
Hukumar SSS ta gurfanar da su a gaban kotu tun a watan Satumbar 2025 kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ƙera bama-bamai na gida da kuma wasu laifuka masu alaƙa da ta’addanci.
Daga karshe dai, kotun ta yanke musu hukuncin daurin rai da rai.
You must be logged in to post a comment Login