Labarai
’Yan bindiga sun kashe shugaban APC na Karamar Hukumar Dekina a Jihar Kogi

Wasu ’yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Dekina a Jihar Kogi, Ishaq Yunusa, tare da yin garkuwa da wani mutum da ke cikin motarsa.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis a kan titin Itobe zuwa Ochadamu, kusa da Ojuwo Olijo, a Karamar Hukumar Ofu ta jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kogi, ASP Afusat Saliu, ta tabbatar da lamarin, inda ta ce ’yan bindigan sun fito daga cikin daji suka bude wa masu ababen hawa wuta.
Ta ce an gano motar Ishaq Yunusa, kirar Toyota Corolla mai launin shudi, a tsaye a gefen hanya, inda aka same shi a cikinta ya mutu, yayin da aka tafi da wanda ke tare da shi zuwa cikin daji.
’Yan sandan sun ce suna hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen binciken dazuzzukan yankin domin kubutar da wanda aka sace da kuma cafke wadanda suka kai harin.
You must be logged in to post a comment Login