Labarai
DSS ta kama shugaban tsaron gwamnan Adamawa
- Hukuma tsaro ta Nijeriya DSS ta kama Ahmad Umar shugaban tsaron gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da mutane uku
- Ana zargin hakan ya biyo bayan ganin bidiyon ‘yan siyasa na Jihar na zagin shugaban DSS din
- Haka zalika da kuma bayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben kujerar gwamnan Jihar Adamawa
Hukuma tsaro ta DSS ta kama Ahmad Umar shugaban tsaron gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da mutane uku magoya bayan jam’iyyar PDP, sakamakon zargin cin zarafin jam’inta da kuma jami’an hukumar zabe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta DSS ta kama su ne a daren jiya alhamis.
Idan ba’a manta ba dai a baya cikin wani fefen bidiyo an ga wasu fusatattun ‘yan siyasa sun shiga Otal din Green City dake birin Yola, tare da cin zarafin babban jami’in DSS.
Hakan ya biyo bayan bayana sakamakon ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zabe, da dakataccen kwamishinan zaben jihar Hudu Yunusa-Ari ya yi a baya.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login