Labarai
DSS ta sake gurfanar da maitangaran a Kotun Abuja
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sake gurfanar da mutumin nan Husseini Ismaila wanda ake wa lakabi da ‘Maitangaran’ a gaban kotun tarayya da ke Abuja, wanda shi ne mutumin da ya shirya harin masallacin gidan Sarki a nan Kano a shekarar 2014.
Tun da fari lauyan hukumar DSS Mr. E.A. Aduda, ya shaidawa kotun cewa, hukumar DSS ta yi gyara ga takardar kara da ta gabatar, inda ta kara wasu sabbin tuhume-tuhume guda hudu kan wanda ake zargin, inda ya yi fata kotun za ta karantawa wanda ake zargin sabbin tuhume-tuhume da ake yi masa domin ya kare kansa.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta zarge-zargen gaba daya da ake yi masa.
Takaradar karar da hukumar DSS ta gabatarwa kotun ta nuna cewa, Husseini Ismail (Maitangaran) mai shekaru 34, wanda da bakinsa ya amince cewa shi mamba ne na kungiyar Boko-Haram, ya jagoranci wasu tagawayen hare-hare da kungiyar Boko-Haram ta kai Kano ciki har da babban masallacin juma’a na Sarkin Kano a shekarar 2014, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login