Labarai
Duk wanda ba shi da lambar NIN zai fuskanci daurin shekaru 14 – Pantami
Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami, ya ce, duk wani dan Najeriya da ba shi da lambar shaidar zama dan kasa (NIN) zai iya fuskantar daurin shekaru goma sha hudu a gidan gyaran hali.
Dr Isa Ali Pantami ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da kwamitin kula da sadarwa na shugaban kasa ya saba gudanarwa a duk mako.
Ya ce ya zuwa jiya laraba talatin da daya ga watan jiya na Maris,‘yan Najeriya miliyan hamsin da daya ne suka yi rajistar lambar ta NIN.
‘‘Ina tabbatar muku cewa duk dan Najeriya da ya yi sakaci bai mallaki lambar shaidar dan kasa (NIN) ba, to zai iya fuskantar daurin shekaru goma sha hudu, kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin kasar nan’’ a cewar Pantami.
You must be logged in to post a comment Login