Kiwon Lafiya
EASTER:An bukaci yan siyasa da su sanyan bukatun al’umma maimakon cimma manufansu
Shugaban cocin Katolika da ke Abuja, John Cardinal Onaiyekan ya bukaci ‘yan siyasa da suyi koyi da halayen Yesu Almasihu, na sanya bukatun jama’ar su maimakon cimma wata manufa tasu ta daban.
Shugaban cocin katolikan ya bayyana hakan ne, lokacin da yake jawabi, yayin wani taro na musamman da aka shirya kan bikin Easter, wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.
Onaiyekan ya zargi wasu daga cikin ‘yan siyasa da nade hannu suna kallon yadda ake kashe wadanda basu ji ba basu gani a jihohin su.
A cewar sa abin takaici ne ace ire-iren wadannan shugabanni suna kallon yadda al’umma ke cikin tashin hankali, amma sun gaza daukar matakan da suka dace, maimakon hakan sai suka mayar da hankali kan abinda zai kare martabar kujerar da suke kai.
Onaiyekan ya kara da cewa irin wadannan shugabanni ba sune suka cancanta su rike shugabancin al’umma ba, domin kuwa abinda suka sanya a gaba shine cimma wata manufa ta su ta daban, ba wai kishin al’umma da kuma basu kariya ba.