Labarai
ECOWAS da sojojin Mali sun cimma yarjejeniyar sakin Boubacar Keita
Jagororin kungiyar cigaban yammacin Afirka ta ECOWAS da mambobin rundunar sojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun cimma yarjejeniyar sakin hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito shugabannin sojoji sun bayar da shawarar kafa gwamnatin rikon kwarya ta sojoji wacce za ta kwashe shekara uku kafin daukar mataki na gaba.
Sai dai dubban ‘yan kasar ta Mali sun fito kan titunan babban birnin kasar Bamako ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka rika nuna goyon bayansu ga juyin mulkin na baya-bayan nan.
Sojojin da suka kwace mulki a Mali sun ce suna tattaunawa da jam’iyyun adawa da sauran kungiyoyi a kokarin kafa gwamnatin da suke yi.
You must be logged in to post a comment Login