Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

INEC ta sanya lokacin zaben jihohin Bayelsa Imo da Kogi

Published

on

Yayin da zabukan gwamnonin jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi ke Kara gabatowa ita kuwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun tashe-tashen hankula a jihohin.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a yayin wani taron kwamatin tuntunba kan tsaro a shirye-shiryen gudanar da zabuka.

Hukumar zaben dai ta sanya ranar 11 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2023 a matsayin ranakun da za’a gudanar da zabukan jihohin guda uku.

Yanzu haka dai gungun masu tada hargitsi ta hanyar amfani da bundugogi sun yawaita a yankunan lamarin dake tilastawa masu shaguna rufewa yayin da sauran jama’a ke rantawa a na kare don tsira da rayukansu.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!