Labarai
EFCC ta cafke Engr Saleh Mamman kan zarginsa da almundahanar biliyan 22
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta cafke tsohon Ministan lantarki Injiniya Saleh Mamman, kan zargin da ake masa na karkatar naira biliyan 22 da aka ware, domin inganta samar da wutar lantarki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito jami’an EFCC sun yi awon gaba da tsohon Ministan ne jiya laraba, domin amsa tambayoyi a kan yadda makudan kudade suka salwanta.
Rahotonni sun bayyana cewa, ana zarginsa ne da karkata naira biliyan 22 da aka ware domin aikin samar da wutar a Zungeru da Mambilla, inda ake zargin Ministan sun raba kudin tare da wasu manyan jami’an ma’aikatarsa.
You must be logged in to post a comment Login