Labarai
EFCC ta fara bincike kan wasu kuɗin ƙasashen waje da Custom ta kama a Filin Jirgi na Kano

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa EFCC ta fara bincike kan dala $73,000 da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje da Hukumar Hana fasa kwauri watau Custom ta kama a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Hukumar ta EFCC, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da fitar kan kuɗaɗen da aka kama a filin jirgin tsakanin ranakun 8 zuwa 12 ga Agustan bana.
Sanarwar ta ce, kuɗaɗen sun haɗa da dala $73,000, fam £15,957 da Riyal na Saudiyya 827,800, waɗanda ba a bayyana wa hukuma ba kafin jami’an Kwastam su kama su.
Haka kuma, hukumar ta ce, a ranar 12 ga Agusta, 2026, jami’an Kwastam sun kama Haruna Yusuf bayan ya isa filin jirgin a jirgin Ethiopian Airlines, inda aka gano dala $20,000 da fam £15,957 da aka ɓoye a cikin takalman wasanni da ke cikin kayansa.
Mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kwastam na Kano da Jigawa, U. U. Adamu, ya miƙa Haruna Yusuf da kuɗaɗen da aka ƙwato ga EFCC domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da doka ta tanada.
You must be logged in to post a comment Login