Connect with us

Labarai

Kano: Ma’aikatar Sufuri ta musnta ba da izinin yin Acaba a Sabon Gari

Published

on

Ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano, ta musanta batun cewa, ta bayar da izinin gudanar da sana’ar Acaba a yankin Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.

 

Ma’aikatar ta ce takardar da aka fitar a baya ta kasance wani ɓangare ne na nazarin buƙatar da wata ƙungiya ta gabatar, ciki har da tantance bayanan mambobinta, amma ba izini ko lasisi ba ne.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Zaharaddeen Adam Ibrahim, Ma’aikatar ta ce, saboda batutuwan tsaro da kula da zirga-zirgar ababen hawa, ta nemi shawarwari da ƙarin umarni daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano kafin a yanke hukunci kan buƙatar.

 

Ta kuma jaddada cewa dokar da ta haramta aikin Achaba a birnin Kano da kewaye na nan daram, tare da gargadin ƙungiyar da abin ya shafa da sauran jama’a da kada su fara aikin bisa wasiƙar da aka bayar a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!