Labarai
EFCC za ta gurfanar da Emifiele ranar Laraba
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, za ta gurfanar da tsohon gwamnan CBN Mista Godwin Emefiele a gaban Kotu gobe Laraba saboda ba da izinin buga sabbin takardun naira na sama da miliyan 684 akan sama da naira biliyan 18.
Tun da fari dai an tsara gurfanar da Godwin Emefiele a ranar 30 ga watan Afrilu da ya gabata amma aka ɗage ranar bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kotun da kuma ɓangarorin biyu.
Hukumar EFCC ta yi zargin Emefiele ya yi burus da umarnin kotu da nufin jefa jama’a cikin mawuyacin hali lokacin aiwatar da tsarin sauya takardun naira da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.
EFCC ta kuma zargi Emefiele da ba da izinin cirar sama da naira biliyan 124 daga asusun bai ɗaya na ajiyar kuɗaɗen shu=iga na gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login