Labaran Wasanni
EFL Cup: Manchester United ta yi rashin nasara a hannun West Harm United

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham United ta doke Manchester United har gida a gasar cin kofin ‘ EFL cup’ na kasar Ingila.
West Ham ta samu nasarar akan Manchester United da ci 1-0 a wasan da ya gudana tsakanin su Laraba 22 ga watan Satumbar shekarar 2021.
Dan wasan tawagar West Ham United Manuel Lanzini ne ya jefa kwallo 1 a ragar Manchester United a minti na 9 da fara wasan na farkon Rabin lokaci.
Kwallo daya da dan wasan ya zura ,ita ta baiwa tawagar sa Nasara bayan da aka tashi wasan a minti na 95 ciki har da karin lokaci.
You must be logged in to post a comment Login