Kaduna
El-rufai ya dakatar da ɗaya daga cikin masu naɗa Sarkin Zazzau
Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu, wanda shi ne jagoran masu naɗa sarki a masarautar.
Dakatarwar ta biyo bayan amsa takardar tuhumar da aka aike ma sa.
Gwamnatin ta aikewa sauran masu naɗin Sarkin guda huɗu takardar tuhuma da ake buƙatar su bayar da amsa.
Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar ta fitar.
Ta hannun babban sakataren ma’aikatar Musa Adamu a madadin kwamishina Jafaru Sani.
Labarai masu alaka:
Obasanjo ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar sarkin Zazzau
Za a yi jana’izar Sarkin Zazzau da ƙarfe 5 na yamma
Masu naɗin Sarkin guda huɗu da ake dakon amsar tuhumar sun haɗar da Limamin Gari Alhaji Dalhatu Kasimu, da Limamin Kona Muhammad Sani Aliyu.
Gwamnatin Kadunan tana zargin masu naɗin Sarkin da ƙin mutunta gayyatar da ma’aikatar ƙananan hukumomi da masaurautu ta yi musu a baya.
You must be logged in to post a comment Login