Labarai
El-Rufai ya shigar da sabuwar kara kan hukumar ICPC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya shigar da sabuwar kara kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, yana neman diyyar Naira biliyan 10.
El-Rufai na zargin hukumar da hana matarsa, Aishatu Asabe da dansa, Abba El-Rufai, ganinsa yayin da yake tsare a hannun hukumar.
A ƙarar, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta tabbatar da cewa hakkokinsa na dan Adam suna nan daram duk da kasancewarsa a tsare.
Ya kuma ce hana iyalansa ganinsa ya hana su kai masa abinci, magunguna da sauran abubuwan bukata.
El-Rufai ya kuma nemi kotu ta ba shi damar ganin iyalansa da lauyoyinsa a lokacin da yake tsare.
You must be logged in to post a comment Login