Connect with us

Labarai

Adeleke ya sake lashe zaben Gwamnan Jihar Osun

Published

on

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar, bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

 

Adeleke ya samu kuri’u 511,067, inda ya lashe kananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar. Dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya zo na biyu da kuri’u 444,815, bayan ya lashe kananan hukumomi 9.

 

Jami’in da ya bayyana sakamakon, Mataimakin Shugaban Jami’ar Federal University Oye-Ekiti, Farfesa Joshua Ogunwole, ya ce Adeleke ya cika sharuddan doka, don haka ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma ya dawo kan kujerar gwamnan jihar Osun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!