Labarai
Ɗan takarar ADC ya taya Adeleke murnar lashe zaben gwamnan Osun

Ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a zaɓen gwamnan Osun, Najeem Salaam, ya taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake zaɓarsa, yana mai cewa sakamakon zaɓen ya nuna cewa dimokuraɗiyya ta yi nasara.
Salaam ya ce ya kamata a mutunta zaɓin al’ummar jihar, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayin siyasa ba.
Ya kuma bayyana cewa siyasa ba ta kamata ta zama batun yaƙi ba, yana mai kira ga dukkan ‘yan siyasar jihar da su kare zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Salaam ya buƙaci Adeleke ya yi amfani da wa’adinsa na biyu wajen gyara wuraren da gwamnatinsa ta yi kasa a gwiwa, tare da ƙarfafa nasarorin da aka samu.
Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya yi mulki ne domin amfanin dukkan al’ummar Osun, ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.
A zaɓen, Adeleke ya samu ƙuri’u 511,067, yayin da ɗan takarar APC, Oyebamiji, ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC kuma ya samu 17,180.
You must be logged in to post a comment Login