Labarai
ENDSARS: Za a hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamon zargin kisan kai
Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin yayi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.
Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.
Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Gombe Kaduna da Kogi da kuma Kwara.
Sauran sune jihohin Lagos da Ogun da kuma jihar Rivers.
You must be logged in to post a comment Login