Labarai
Fadar shugaban kasa ta gargadi kasashen Turai
Fadar shugaban kasa ta gargadi kasashen Amurka da Burtaniya da kuma tarayyar turai da su guji tsoma baki cikin lamuran da ya shafi kasar nan,musamman zargin take hakkin bil adama.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka ta cikin shirin gidan talabijin na Channels mai taken: Politics Today’ kan zargin da kasasen ke yi ga kasar nan na take hakkin bil
adama.
Mr Femi Adesina ya ce Najeriya kasa ce mai ‘yanci saboda haka ko da wasa ba za ta bari wata kasa ta rika tsoma mata baki cikin harkokinta na cikin gida ba.
Da aka tambaye shi kome zai ce game da samamen da jamian hukumar tsaro ta DSS su ka kai kotu da kuma kama mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore, Femi Adesina ya ce, Najeriya ba kasa ce da ta ke amsar umarni daga kasar Amurka ko Burtaniya ko kuma tarayyar turai ba.