Labaran Kano
Fadar shugaban kasa ta kaiwa Sarkin Kano ziyarar ta’aziyya
Tawagar jami’ai daga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo ziyarar ta’azyya ga mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II yau Asabar a fadarsa.
Tawagar karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari ta zo Kano ne domin yin ta’aziyya ga Sarkin na Kano, bisa rasuwar kawunsa Ambasada Ado Sanusi Dan Iyan Kano mai murabus.
Har ila yau tawagar ta mika takardar jajantawa daga shugaban kasa zuwa ga Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wadda ta bayyana alhininta kan rashin marigayin.
Sannan fadar shugaban kasa ta ce rashin Ambasada Ado Sanusi ba karamin rashi ne ga al’umma ba, duba da irin gudummuwar da ya baiwa kasar nan a lokacin da yana ambasada.
Tawagar fadar shugaban kasar ta hadar da mataimakin shugaban kasa na musamman a kan yada labarai Malam Garba Shehu da ministan tsaro General Bashir Salihi Magashi da kuma Ministan Noma Malam Sabo Nanono.
Sarkin Kano da Hakimai da sauran ‘yan majalisar sarki ne, suka tarbi tawagar Fadar shugaban kasar.
Karin hotuna a lokacin ziyarar.
Tun da farko dai tawagar ta kai makamanciyar wannan ziyara ga fadar gwamnatin Kano, inda tayi ta’aziyya ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan wannan rashi.
A shekarar 1963 ne, marigayi Ambasada Ado Sanusi yayi murabus daga sarautar Dan Iyan Kano, inda ya fara aiki da ma’aikatar lura da kasashen waje ta Najeriya.
Kafin rasuwar marigayin yayi Ambasadan Najeriya a kasashen Morocco da Saudi Arabia, da Indonesia da kuma kasar Iran.
Karin labarai:
Kano: zan tsoma baki kan rikicin Sarkin Kano da Ganduje – Buhari
You must be logged in to post a comment Login