Siyasa
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cin hanci da ake yiwa Abba Kyari
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cin hanci da ake yiwa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, tana mai zargin cewa, fusatattun ‘yan siyasa ne da ba su da ta cewa sakamakon wadaka da dukiyar jama’a da su ka yi tsawon lokaci suka kisa maganar da ba ta da tushe balle makama.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Sanarwar ta bayyana zargin da cewa shifcin gizo ne kawai da bashi da makama domin Abba Kyari bai ta ba ganawa da mutumin da ake zargin cewa ya bukaci cin hanci daga gareshi ba.
A baya-bayan nan ne dai wata jarida ta ruwaito cewa Abba Kyari na karbar cin hanci a wajen masu neman kwangila.
Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar ya kuma zargi jaridar da ta yada labarin da rashin kwarewar aiki, yana mai cewar duk da nakaso da rashin hujja da labarin ke dauke da shi amma ta yi gaban kanta wajen yadawa.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar ya kuma ce, yayin da zabe ke karatowa ‘yan siyasa da basu da goyon bayan jama’a na ta kokarin amfani da baragurbin ‘yan jarida wajen bata sunan fadar shugaban kasa don biyan bukatun kansu na siyasa.
Sanarwar ta kara da cewa abin dariyar ma shine yadda aka ce wai an Abba Kyari ya nemi cin hancin naira miliyan ashirin da tara wajen kwangilar shigo da motoci kirar Hilux guda goma sha biyar ga fadar shugaban kasa, a cewar sa, tsakanin shekarar dubu biyu da goma sha shida zuwa dubu biyu da goma sha bakwai fadar shugaban kasa ba ta sayi motocin Hilux guda goma sha biyar ba, babu kuma inda hakan ya ke a cikin kasafin kudin shekarun.