Labaran Wasanni
Farashin Mbappe ya kai Yuro miliyan 200 – PSG
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta saka kudi Yuro miliyan 200 kan gwarzon dan wasa Kylian Mbappe ko da zai bukaci canja sheka idan kwantiraginsa ya kare.
Makomar dan wasan ta ta’allaka a gareshi ne, bayan da ya nuna wa duniya kwarewar sa a fagen wasan kwallon kafa.
Mbappe ya kasance zakaran dan wasa a ranar 16 ga watan Fabrairu inda ya samu zarrar jefa kwallo uku a ragar Barcelona.
Barcelona dai tasha kashi a hannun PSG da ci hudu da daya a ranar Talatar da ta gabata a gasar zakarun nahiyar Turai.
Kwantiragin Mbappe a PSG zai kare ne a watan Yunin shekarar 2022, hakan zai bashi damar sabunta kwantiragin ko kuma ya canja sheka.
Kawo yanzu dai Mbappe mai shekaru 22 bai furta komai ba kan makomar tashi idan shekarar ta 2022 ta zo, yayin da kuma manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya ke cigaba da zawarcin dan wasan kamar su kwaceshi.
Kungiyoyin sun hadar da Liverpool da Manchester City da Real Madrid da kuma Juventus.
You must be logged in to post a comment Login