Labarai
Fasinjojin Azman Air daga Abuja zuwa Kano sun koka
Wasu ƴan jihar Kano sun koka kan zargin tauye musu haƙƙi daga kamfanin jirgin sama na Azman.
Fasinjoji ne da suka biya kuɗi domin jirgin ya kawo su Kano daga Abuja a yammacin Jumu’a.
Sai dai bayan da aka karɓi kayayyakinsu domin shirin tashi, sai aka basu uzrin cewa ba zasu samu tashi ba, a cewar wani daga ciki.
Haka aka riƙa yi har sau uku, daga bisani ne kuma aka sanar da su cewa kamfanin jirgin ya soke jigilarsu.
Karin labarai:
Hukumar bincike kan hadarin jiragen sama ta fitar da rahoto kan jirgin da ya fadi a Legas
An bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane a Kano
Alhaji Ali Babba Ɗanagundi yana cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Yace, “An ce su zauna, sun zauna har sau uku ana ɗaga tashinsu, kuma ƙarshe an ce an soke tashin jirgin baki ɗaya, ba tare da ba su wani uzri ba”.
Ita ma Ralliya Ado Jibril da ke cikin fasinjojin ta ce, ta shafe awanni biyar a filin jirgi, kuma ƙarshe an ce da ita an soke tashin jirgin.
Wasu fasinjojin dai sun zargi cewa kamfanin zai juya akalar jirgin ne domin kai fasinja zuwa Legas.
Sai dai koda muka tuntuɓi shugaban kamfanin na Azman Air, Alhaji Sulaiman Lawan ya ce, ba haka lamarin ya ke ba.
A cewar sa, jirgin ya zo Kano tun ƙarfe biyar da niyyar zai koma Abuja domin dawo da fasinja amma hakan bai samu ba saboda matsalar da ya samu.
Ya ci gaba da cewa, yanzu haka ana tsaka da gyara jirgin domin gobe ya je ya yi jigilar fasinjojin.
Dangane da rashin yin cikakken bayani ga fasinjojin Alhaji Sulaiman ya ce, ba haka bane, domin kamfanin yana biyayya ga doka wajen kyautata alaƙarsa da fasinjojinsa.
“Wannan kamfani kuɗi ya ke nema, fasinjojin nan kuɗi suka biya, ka ga ba zamu ce ba su da kuɗi ba” inji Alhaji Sulaiman.
Game da masu zargin cewa an juya akalar jirgin zuwa Legas, shugaban kamfanin ya ce babu gaskiya a ciki har ma ya ce, “Na rantse da Allah wanda ya halicce ni jirgin nan yana Kano ana gyaransa”.
You must be logged in to post a comment Login