Labarai
Fayemi: Ayyukan ta’addanci sun ragu a mulkin Buhari idan aka kwatanta da shekarun baya.

Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce, ayyukan ta’addanci sun ragu sosai a Najeriya tun bayan da shugaba Buhari ya fara mulki a shekara ta 2015
Fayemi wanda tsohon minister ne a gwamnatin Buhari a zangon farko duk da yake a yanzu jama’a da daman a zama cikin zullumi sakamakon matsalar tsaro amma an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da halin da kasar ke ciki kafin zuwan Buhari a shekarar 2015.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen bullo da sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen dakile matsalolin da kasar nan ke fuskanta
Gwamnan na Ekiti ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ya halarta a Lagos a ranar asabar.
You must be logged in to post a comment Login