Labaran Wasanni
FIBA ta zabi Chamberlain Oguchi a matsayin gwarzon dan wasa
Hukumar shirya kwallon Kwando ta FIBA Afrika ta fitar da sunan tsohon dan wasan kungiyar kwallon Kwando ta kasa D’Tigers a matsayin kwarzon dan wasan Najeriya na tsawon shekaru goma da suka gabata.
Hukumar ta fitar da suna Chamberlain Oguchi, a matsayin gwaron dan wasan na kwallon Kwando a Najeriya a tsawon shekaru goman da suka gabata.
Hakan na kunshe ta cikin jerin sunayan ‘yan wasan da suka nuna hazaka a kasashen su karo na biyu da hukumar ta FIBA Afrika ta fitar.
Ragowar ‘yan wasan da hukumar ta fitar da sunayan nasu tsawon shekaru goman sun hadar da kyaftindin kungiyar na yanzu Ike Diogu da Orlando Magic da Al-Farouk Aminu.
An fitar da sunayan ‘yan wasan na Najeriya ne cikin ‘yan wasan Afrika 55 da hukumar kwallon kwandon ta Afrika FIBA ta fitar da suka nuna hazaka a kasashensu daga shekarar 2010 zuwa 2020.
Oguchi dai ya taba zama gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2015 bayan kammala gasar kwallon Kwando data gudana a kasar Tunisia wanda ya nuna hazaka a gasar.
Yan wasa goma da hukumar ta FIBA Afrika ta fitar da sunayan su a yankin na Afrika sun hadar da dan wasan kasar Morocco’s Abdelali Lahrichi da ‘yan wasa biyu daga kasar Senegal Memphis Grizzlies da Gorgui Dieng da kuma yan wasa hudu daga kasar Tunisian da suka hadar da Makram Ben Romdhane da Salah Mejri da Angolans Eduardo Mingas da Carlos Morais.
Sauran sun hadar da dan wasan kasar Ivory Coast Souleyman Diabate da ‘yan wasan Nigerian trio Diogu da Aminu, da kuma Oguchi.
You must be logged in to post a comment Login