Kiwon Lafiya
Fiye da kaso Saba’in na yara ‘yan Najeriya ba su da takardun haihuwa – UNICEF
Asusun tallfawa kananan yara na majalisar dinkin Duniya UNICEF ya ce akalla kaso Saba’in da bakwai na yaran kasar nan da basu wuce shekaru biyar ba ba su da takardun shaidar haihuwa ba.
Shugaban Asusun a jihar Enugu, Victor Atuchukwu ne ya bayyana hakan, A taron bayar da horo ga jami’an lafiya Saba’in da biyar da suka fito daga kananan hukumomi Ashirin da daya.
Taron dai ya mai da hankali kan yadda za’a rinka wayar da kan iyaye game da muhimmamcin samarwa ‘ya’yan su takardar shaidar haihuwa a Asibiti.
Victor Atuchukwu, ya kuma ce yana da kyau kowanne yaro a Najeriya ya mallaki takardar tun kafin girma ya riske shi.
Ya kuma ce, idan ba’a yi wa yaro takardar haihuwa ba tun yana yaro, to kuwa za su ceji dan yatsa idan suka girma sakamakon rashin takardar.
You must be logged in to post a comment Login