Connect with us

Labarai

Fiye da mutum 80 sun ɓata bayan hare-haren ƴan bindiga

Published

on

Fiye da mutum 80, akasarinsu mata sun ɓace bayan da ƴanbindiga suka ƙaddamar da hare-hare biyu a wasu jihohin Arewacin Najeriya a ranakun ƙarshen mako.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa a ranar Asabar, ƴanbindiga sun sace aƙalla manoma 47 yayin da suke gona a jihar Neja inda kuma a jiya Lahadi, aka yi garkuwa da mata 40 a jihar Zamfara.

Ƴanbindiga na yawan kai munanan hare-hare kan ƙauyuka inda suke halaka mutane tare da ƙona gidajensu bayan sun sace musu dukiya.

Wata majiya a jihar Neja ta ce manoma 47 galibinsu mata, an sace su a gonakinsu da ke Rimi a yankin Mariga na jihar Neja.

Wani rahoton tsaro da aka shirya wa kungiyoyin jin kai, wanda AFP ta gani, ya tabbatar da faruwar hare-haren amma bai bayyana adadin mutanen da aka sace ba.

Matan da aka sace jiya Lahadi an yi garkuwa da su ne a Yargada da ke Gusau a jihar Zamfara, a cewar wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Dinkin Duniya, wanda AFP ta gani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!