Labarai
Za mu koma teburin sulhu da Iran- Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce, yana sa ran Amurka da Iran za su koma teburin tattaunawa a makon da muke ciki, duk da cewa ya yi watsi da shawarar Iran ta tsagaita wuta na kwanaki bakwai da kuma sake bude mashigin ruwan Hormuz.
Iran ta gabatar da shirin ne a Majalisar Dinkin Duniya, inda ta nemi a dakatar da duk wani fada a Gabas ta Tsakiya tare da cika wasu sharudda, ciki har da dage takunkuman tattalin arziki da sakin kadarorinta da aka daskarar. Sai dai Trump ya ce tayin Iran bai yi daidai da yarjejeniyar da yake so ba.
A halin da ake ciki, Iran ta ce ba za ta sauya matsayinta ba, yayin da dakarun juyin juya halin kasar suka sanar da kama wani jirgin karkashin ruwa mara matuki na Amurka a mashigin ruwan Hormuz, suna zargin an yi amfani da shi wajen leken asiri.
You must be logged in to post a comment Login