Connect with us

Labarai

CBN ya gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a Kano

Published

on

Babban bankin ƙasa CBN, ya gargaɗi al’ummar ƙasar nan kan su guji wulaƙantabtakardun kuɗi ko kuma yin duk wani abu da ka iya lalata su, domin magance kashe maƙudan kuɗaɗe wajen buga wasu da gwamnati ke yi.

Daraktan sashen harkokin kuɗi na babban bankin Dakta Adetona Adedeji, ne ya yi wannan gargaɗi yau Litinin yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da CBN ɗin ya yi a kasuwannin Sabon Gari da ta Galada da kuma kasuwar Mayanka watau Abbatuwa a nan Kano.

 

Dakta Adedeji Adetona, wanda ya samu wakilcin jami’i a sashen kula da buga harkokin kuɗi da kuma bayar da su, Alhaji Ibrahim Yahaya, ya ce, an ɗauki matakin yin gangamin ne domin jan hankalin mutane wajen daina lalata kuɗi kasancewar su wani ɓangare na martabar ƙasar nan, don haka su ke raba wa mutane jakar zuba kuɗi domin alkinta su.

 

Yace, ”Gwamnati na kashe kudade masu yawa wajen buga sabbin takardun kudi, saboda takardun da ake buga kudin da su na musamman ne, haka ma Inki da dukkan abubuwan da ake amfani da su, don haka mu ke kira ga mutane da su daina barin kudi su na lalacewa.”

 

”Ya kamata mutane su daina barin kudi su na jikewa ko ajiye su a waje mai danshi ko kuma cukuikuye su, shi ya sa muka kirkiri sabbin jaka wadda ake iya adana kudi, a matsayinku na yan kasuwa za mu raba muku su kyauta, amma ba za mu iya bai wa kowa ba, don haka duk wanda bai samu ba sai ya je ya sayi wadda ke kama da wannan domin rika adana kudadensa.”

 

A nasa ɓangaren shugaban kasuwar Galadima, Malam Mustapha Shu’aibu Sulaiman, ya yaba wa babban bankin na ƙasa CBN bisa faɗakarwar, tare da yin kira da su hana bankuna ci gaba da bai wa mutane lalatattun takardun kuɗi.

 

Shugaban kasuwar ta Galadima, ya ce, a ”A kullum idan muka karbo kudi daga Bankuna, mu na samun lalatattu a ciki, don haka mu na kawo muku wannan korafi da ku haka bankuna ci gaba da fito da kudin da su ka lalace, domin bai kamata a ce kudi sun lalace ba amma kuma idan an kai su banki su sake fito da su”.

 

Mu na godiya sosai ga CBN bisa wannan fadakarwa da su ka yi mana, kuma, za mu tabbatar da cewa mun isar da ita ga sauran yan kasuwa domin su ma su fadaka.

 

Babban bankin na ƙasa CBN, zai ci gaba da za gayawa manyan kasuwannin Kano da su ka haɗa da ta Dawanau da Ƴan Lemo da Ƴan Kaba da kuma kasuwar Tarauni, domin ci gaba da faɗakar da mutane kan daina lalata takardun kuɗi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!