Connect with us

Labarai

Sojojin Najeriya na fama da karancin ma’aikata da kayan aiki – Zulum

Published

on

Gwamman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, yace, Sojojin kasar nan na fama da karancin ma’aikata da kayan aiki.

Ya kuma ce, hakan ne ke kawo nakasu ga yakin da suke da ‘yan Boko Haram da ‘yan ta’adda a fadin kasar nan.

Babagana Zulum, ya bayyana haka ne a hirar sa da gidan talabajin na Channels a jiya Laraba 7 ga watan Yulin 2021.

Gwamna Zulum, ya ce a tsawon shekarun 40 da suka wuce a baya Sojin kasar nan na da wadatattun makamai da jami’ai, sai dai yanzu akwai kalubale da dama ciki har da na rashin ma’aikata.

Zulum, ya kara da cewa akwai bukatar samar wa da jami’an Sojin sabbin makamai na zamani da zai taimaka musu wajen cimma manufar da suka saka a gaba, sabanin yadda a yanzu suke amfani da makaman da aka siye su tun tsawon shekaru 40.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!