Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

An sake samun bullar cutar Coruna Virus karo na uku a kasar nan

Published

on

 

Gwamnatin jihar Lagos, ta sanar da sake bullar cutar Corona Virus, a jihar bayan samun wata mata mai  shekaru 30, da ke  dauke da ita bayan  dawowar ta  kasar nan daga Ingila, sakamakon ziyarar kwana 10 da tayi a can.

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Akin Abayomi, ne ya bayyana wa manema labara a wani taron ‘yan jaridu da ya gudana a yau in da yace zuwa yanzu haka karo na uku ke nan da ka samu bullar cutar a jihar.

Akin Abayomi, ya kara dacewa matar wacce yanzu haka an killace ta, ta nuna alamun rashin lafiya na kamuwa da cutar ta Covid 19, da suka hada da tari, zazabi mai zafi da makamantan su.

Labarai masu alaka.

Hisbah ta gano maganin Coronavirus

Daliban Kano a Sudan sun nemi a dawo dasu gida saboda Coronavirus

Kwamishinan yace bayan kwakkwaran bincike an samu matar da kamuwa da cutar, wadda ita ce karo na uku da aka samu bullar cutar a jihar ta Lagos, da a yanzu haka ya tabbatar da cewar ministan lafiya na kasa  Osagie Ehanire, na gudanar da taron manema labarai yanzu haka don karin haske akan lamarin.

Akin Abayomi, yace matar ta sauka a kasar nan ne, a birnin na Lagos ranar 13 ga watan Maris, an kuma killace ta daga cikin iyalanta, kasancewar ba wai ana zargin ta da cutar bane  an tabbatar tana dauke da cutar.

Zuwa yanzu haka tana killace a Asibitin cututtuka masu yaduwa dake Yaba. Hakan dai na zuwa ne  kwanaki kadan bayan da jihar ta Lagos, ta bayyana cewa mai duke da cutar da aka samu na biyu ya warke daga cutar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!