Labarai
Fiye da yan tada kayar baya 1,300 sun mika wuya ga sojoji
Shalkwatar tsaron Nijeriya, ta bayyana cewa ‘yan ta-da-ƙayar-baya da iyalansu su feye da dubu daya da dari uku da talatin da biyu sun miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin kai a yankin Arewa maso Gabas cikin makonni biyu da suka gabata.
Daraktan harkokin yaɗa labaran na shalkwarat Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan.
Ya ce, ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa wuya sun ƙunshi magidanta dari biyu da ashirin da biyu da mata dari hudu da goma sha daya sai ƙananan yara dari shida da casa’in da tara.
Shalkwatar tsaron ta kuma ce, ta na ci gaba da tantance ɗaruruwan ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa wuya a tsawon mako biyun, kafin ɗaukar mataki na gaba a kansu.
Haka kuma, shalkwatar ta ce, rundunar ta samu nasarar kashe wasu yan tada kayar baya guda 8, an kuma kama mutanen da ake zargin su ne suke kai musu kayan buƙata su 5 a dai-dai lokacin da suka kuɓutar da wadanda aka sace su 19.
You must be logged in to post a comment Login