Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu daukaka kara kan umarnin amfani da katin wucin gadi- INEC

Published

on

Hukumar INEC, ta ce, za ta daukaka kara kan batun umarnin da kotun tarayya ta bayar kan ta amince da yin amfani da katin zabe na wucin gadi a yayin zaben gwamnoni da ke tafe.

A wani sako da hukumar INEC ta wallafa a shafin ta na Twitter ta ce, ta karbi kwafin takardar umarnin babbar kotun tarayyar kan batun ba da damar yin zabe ga masu katin zabe na wucin gadi.

A jiya Alhami ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bai wa hukumar zabe INEC umarnin amincewa da batun kada kuri’a, ga masu katin zabe na wucin gadi a zaben gwamnoni da ke tafe.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya bada umarnin biyo bayan korafin wasu yan Nijeriya kan rashin samun katin zaben su na din-din-din, wanda hakan ke nuna cewa ba za su samu damar yin zaben bana ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!