Labarai
FOMWAN:Ta ja hankalin gwamnonin Arewa kan batun almajirci
Kungiyar mata musulmi ta kasa FOMWAN ta bukaci gwamnoni Arewa da su maida hankali wajen magance matsalolin almajirci a matsayin wani babban batu da za’a magance.
Kungiyar ta bukaci tallafin gwamnonin arewa da su tabbatar da wasu shirye-shirye da zai taimakawa wadannan almajirai kauracewa barace-barace akan manya titiuna.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa na bayan taron da kungiyar ta gabata karo na 34 da aka gudanar a Katsina, aka kuma baiwa yan jarida kwapin takardar.
Taron dai ya tattauna batutuwan da suka shafi inganta muhalli ,matsalolinsu da kuma tafiyar da cigaban kasa’
Majalisar dattijai ta kawo kudirin zamantar da illimin tsangaya
Sanarwar mai dauke da sa hannu Amirar kungiyar Hajiya Halima Jibril da jami’a mai yada labarai Dr Sumaye Fadimatu Hamza sun yi tsokaci kan yadda gwamnati bata baiwa harkar ilimi muhimmanci a kasa baki daya, wanda hakan ke dakushe cigaban kasa.
Sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi shaye-shayen kwayoyi tsakanin mata da matasa wanda wannan ke nuni da wata gazawa a bangaren tarbiyar iyali , yake kuma tauye cigaban al’umma da cigaban kasa.