Kiwon Lafiya
Gamayyar kungiyar jami’an ‘yan sanda sun koka da nuna halin ko in kula da ake yi musu
Gamayyar kungiyar jami’an ‘yan sanda masu ritaya da wasu hukumomin tsaro sun zargi majalisar dattawan kasar nan da nuna halin ko in kula kan halin da suke ciki.
Wannan korafi ya biyo bayan jinkirin da majalisun dokokin kasar nan su ka yi na cire su daga cikin tsarin Fanshon taimakekeniya da ake kira PENCOM.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar jami’an ‘yan sandan ta bukaci majalisun dokokin kasar nan da su sauya dokar ta shekarar 2014, Kasancewar ta tsame jami’an ‘yan sandan kasar nan da sauran jami’an tsaro daga cikin tsarin.
Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan kammala taron hadin gwiwa da ya hadar da hukumar hana asa Kwauri ta kasa Custom da hukumar lura da shige da fice ta kasa Immigration da sauran hukumomin tsaro, tana mai cewa bayan sauraron ra’ayoyin jama’a da majalisun dokokin kasar nan suka yi tun watanni 7 da suka gabata kan kudurin dokar, har ya zuwa yanzu babu wani abu da aka yi.
A zanatawarsa da manema labarai bayan kammala taron Sakataren kungiyar na kasa Silvanus Basadeimbo cewa ya yi kungiyar ta su ta bi duk wasu hanyoyin lalubo bakin zaren, amma hakan ya gaza cimma ruwa, yana mai cewa matakin karshe da kungiyar za ta dauka shi ne, zanga-zangar lumana.