Kiwon Lafiya
Ganduje ya bukaci hadin kan iyayen yara wajen Allurar Rigakafi
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci iyayen yara da su baiwa jami’an lafiya hadin kai yayin da ake aikin rigakafin zazzabin cizon sauro, wanda ake gudanarwa a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yau, lokacin da yake zagayawa cibiyoyin da ake gudanar da aikin a wasu asibitoci a karamar hukumar Kura, don duba yadda rigakafin ke gudana.
Gwamna Ganduje kara da cewa maganin rigakafin zai taimaka wajen rage hatsarin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da ake samu a lokacin damuna.
Labarai masu Alaka.
Ana ci gaba da duba marasa lafiya ta wayar hannu a Kano
Gwamnatin Kano za ta yi rigakafi ga yara sama da miliyan 3
A na sa jawabin shugaban hukumar yaki da cutar mai karya garkuwar jiki a nan Kano Dr Sabitu Shanono, ya yi bayani kan magungunan da za a raba a kananan hukumomin da suka hada da na karin jini da na karin kuzari, sai na kariya daga zazzabin cizon sauro.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa gwamna Abdullahi Ganduje ya kuma ziyarci asibitin karamar hukumar Garun Mallam domin duba yadda ake gudanar da aikin.
You must be logged in to post a comment Login