Labarai
Babu gudu ba ja da baya kan gyara gidaje da filaye mallakin gwamnati – Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano tace, babu gudu ba ja da baya akan yunkurinta na gyara duk wasu gidaje ko filaye mallakin gwamnati wadanda ba’a amfani dasu a ko ina suke domin sake ingantasu ta yadda zasu rika samarwa da gwamnati kudaden shiga.
Kwamishinan sharia kuma Atoni janar na Kano Barista Lawan Abdullahi Musa ne ya bayyana hakan a yau a ya yin zantawarsa da manema labarai.
Lawan Abdullahi ya kara da cewa, ya yi mamaki yadda kungiyar ma’aikatan kotu suka gurfanar da gwamnati a gaban babbar kotun Kano kasancewar suna da masaniya kan yadda tsarin shigar da kara wadda ta shafi al’amuran albashin ma’aikata yake da shi, amma suka gurfan ar da gwamati a gaban kotun.
Haka kuma kwamishinan yace kotun da’ar ma’aikata ce kadai keda hurumin sauraron karar da kungiyar ma’aikatan Kotuna suka shigar a babbar kotun jiha kan batun zabtare musu albashi da gwamnati ta yi amma gwamnatin zata yi biyayya da hukuncin Kotun.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewa Barista Lawan Abdullahi na cewa gwamnatin Kano ta sauyawa kamfanin buga jarida na TRIUMPH guri zuwa rukunin gidaje na SheIkh Isyaka Rabiu domin cigaba da gudanar da ayyukansu a can.
You must be logged in to post a comment Login