Labarai
Ganduje ya dakatar da karin kudin dutse da aka yi mana – Kungiya
Kungiyar direbobin tifa ta kasa reshen jihar Kano ta bukaci gwamnatin Kano data dakatarda karin kudin dutse da wasu kamfanonin kasar Sin dake sarrafa duwatsu sukayi musu a nan Kano da kusan kaso arba’in cikin dari batare da sun nemi ji daga bakin kungiyar ba.
Shugaban kungiyar Direbobin Tifa ta jihar Kano Kwamared Mamuni Ibrahim Takai ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai kan batun karin kudin da kamfanonin suka yiwa masu siyan dutsan domin sanarwa da gwamnatin Kano.
Mamuni Ibrahim Takai ya kara da cewa wannan karin da kamfanonin suka yiwa dutsen babu makawa zai haddasa tashin farashin dutsen a yanzu baya ga tsada da kwangila zata kara saboda karin kudin, don kuwa shima talaka gini zai gagareshi.
Shugaban Kungiyar Mamuni Takai yace abun takaicin shine yadda al’ummar Kano suke tarawa wadannan kamfanoni miliyoyin kudade kuma duwatsun da suke sarrafawa suna siyarwa da jama’a na ‘yan Kano ne kuma ’yan Kano ne suke siya don suyi amfani dashi.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito shugaban kungiyar na kira ga gwamnati da ‘yan majalisar Kano harma da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da su takawa yunkurin kamfanonin birki domin mutane na cikin mawuyacin hali a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login