Labarai
Ganduje ya gabatar da dokar kare kananan yara ta bana a gaban majalisar dokoki
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar dokokin jihar wasiƙar neman sahalewa dokar kare ƙananan yara ta bana.
Shugaban majalisar dokokin Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Litinin.
Da yake karanta wasikar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya buƙaci amincewar mambobin majalisar domin sanya buƙatar cikin batutuwan da za a tattauna a zamanta na gaba.
You must be logged in to post a comment Login