Labarai
Ganduje ya gargadi fursunoni su guji aikata laifuka
Shugaban gidan gyaran hali na Goron dutse Magaji Ahmad Abdullahi ya bukaci masu laifin da gwamnan Kano ya yi wa afuwa su kasance al’umma nagari tare da gujewa abinda zai sake dawo dasu gidan a matsayin masu laifi.
Magaji Ahmad Abdullahi ya bayyana hakan ne a yau ya yin da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ke afuwa mutane 29 da suka cancanci a biya musu tara.
Ya kuma Kara da cewa dama mutane 43 ne za’a biya wa tarar inda 14 daga cikin su yan’uwansu suka biya musu Sai kuma 29 da Gwamnan ya yi wa afuwa.
Da yake jawabi gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce in akayi laakari da Zama na gari da wasun su ke yi yayin barin su gidan gyaran halin hakan na nuna cewa ana samun nasara
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Gwamnan ya kuma bukaci su da su kasance alummar da zaa rika alfahari dasu yayin barin su gidan gyaran hali.
You must be logged in to post a comment Login