Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya gargadi makarantu masu zaman kan su kan karin kudi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata tsayar da jarrabawar zangon karatu na uku a makarantun kudi na jihar matukar suka gaza rage kudaden makaranta daga kaso 25 zuwa 30.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Mal. Muhammad Sanusi Kiru ne yayi wannan kiran ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi Aliyu Yusuf ya fitar.

Sanarwar ta ce mafi karancin kudin da ake bukatar makarantun su rage zai fara daga kaso 25 cikin dari na kudaden da kowanne dalibi zai biya, wanda rashin zartar da umarnin gwamnatin zata soke jarrabawar zangon karatu na uku na shekarar 2019 da 2020 ga daliban makarantu masu zaman kansu.

Sunusi Kiru, ya ce hukuncin hakan ya zama wajibi la’akari da yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasa, wanda annobar corona ta janyo ga kowa.

Ya kuma ce, tuni aka samar da kwamitin wucin gadi da zai bibiyi makarantu masu zaman kansu a jihohi hudu zuwa biyar na bibiyar ragin kudaden makarantar ko kuma a soke jarrabawar zango na uku don shiga sabon zango a shekarar 2021.

Sai dai ya ce daga yanzu zuwa daya ga watan Nuwamba mai kamawa matukar makarantun suka gaza aiwatar to kuwa doka zata fara aiki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!