Labarai
COVID-19 : Ganduje ya gargadi Asibitioci masu zaman kan su
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci duk masu cibiyoyin kiwon lafiya na zaman kansu, da su bi umarnin da kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar Corona ke bayar wa domin kare kansu da kuma marasa lafiya.
Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau ya yin taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a dakin taro na Africa House.
Gwamna Ganduje ya ce a jiya an gano wani Asibiti mai zaman kansa yana karya ka’idoji na Covid 19 tare da shigar da marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali ba tare da tura su zuwa ga kwamitin don killace masu cutar da kuma kulawa dasu ba.
A wani bangare kuma gwamnan jihar ya karbi bakuncin dattawan kasuwar Sabongari wadanda suka zo yiwa gwamnan godiya domin rage musu kudin haya a kasuwar saboda kalubalen cutar Covid 19 da ta shafi cigaban tattalin arzikin su da na kasa baki daya.
Wakiliya Zahrau Nasir ta ruwaito ya yin taron majalisar zartarwar gwamnan ya kuma karbi bakuncin shugabannin gudanarwar jami’ar Yusif maitama Sule karkashin jagorancin shugaban jami’ar Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa wanda ya yi karin haske kan nasarorin da aka samu a jami’ar kawo yanzu.
You must be logged in to post a comment Login