Labarai
Ganduje ya kaddamar da shirin kula da baki da hakora a Kano
Gwamnatin Kano ta ce bayar da maganin matsalolin da suka danganci hakora da Baki da kuma bada shawarwari akan yadda mutane zasu kula da lafiyar bakunan su zai taimaka wajen inganta lafiyar a l’ummar jihar Kano.
Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ya yin kaddamar da shirin kula da inganta lafiyar Baki da hakora a babban asibitin Dawakin Tofa anan Kano.
Da yake jawabi mai Martaba sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero ya ja hankalin al’umma Mussama matasa da su guji yin shaye-shayen taba Sigari da sauran nau’inkan kayan maye, kasancewar suna da alaka da kawo cututtuka da ya daganci baki.
Ya Kara da cewa idan al’umma suka kaucewa ta’amali da kayan shaye shayen zasu samu kariya daga cututtukan da ke da alaka da Baki da hakora
Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahrau Nasir, ta ruwaito cewa kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa yace duba da yadda alkaluma suka nuna cewa a fadin duniya mutane biliyan uku da miliyan dari 500 ne ke fama da cututtukan Baki da hakora yasa gwamnatin ta ga dacewar daukar matakan inganta lafiyar bakin al’ummar jihar Kano a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login