Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya miƙa takardar kama aiki ga sabon sarkin Gaya

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa takardar kama aiki ga sabon sarkin Gaya mai daraja ta ɗaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya.

Dakta Abdullahi Ganduje ya bada takardar ama aikin ne a yammacin Litinin a fadar gwamnatin Kano.

“Muna miƙa godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana da aka sanya hannu kan takardar kama aiki ga sabon sarkin Gaya domin kuwa babbar rana ce mai ɗumbin tarihi”.

“Abin godiyar bai wuce yadda masu zaɓen sarki suka yi zaɓe ba tare da kace-na-ce ba wannan ya nuna cewa masarautar Gaya za ta ci gaba da al’amuran ta cikin kwanciyar hankali” a cewar Gwamnan.

Yayin miƙa takardar gwamna Ganduje ya buƙaci sabon sarkin ya mayar da hankali wajen inganta tsaro da harkokin ilimin a masarautar sa.

Da ya ke nasa jawabin sabon sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya ya bukaci waɗanda suka yi takarar sarautar da shi da su haɗa kai da shi don ciyar da masarautar gaba.

“Za mu yi biyayya ga gwamnatin Kano don ciyar da al’amuran jagorancin al’umma cikin gaskiya da amana da kuma don samar da ingantacciyar rayuwa.

Bikin miƙa takardar ya samu halartar manyan jami’ann gwamnatin Kano da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!