Connect with us

Labarai

EFCC: ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji bada gudunmawar karya

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji yin alkawarin karya wajen bada taimakon kayayyakin da zasu taimaka wajen warkar da masu dauke da cutar COVID-19.

Mukadashin hukumar ta EFCC Ibrahim Magu yayi wannan gargadi ‘yan Najeriya cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Tony Orilade ya fitar a Abuja.

Ibrahim Magu ya ce akwai bukatar dake akwai a gargadi  ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su guji amincewa da masu bada taimakon karya kasancewar akwai dokokin da ake bi wajen bada gudunmawa kan cutar COVID-19.

Akan haka ne shugaban hukumar ta EFCC ya kara da cewar, Gwamnatin tarayya ta sanar da asusun bankin da duk wanda yake da sha’awa wajen bada gudunmawa ko taimako da ya sanya a ciki kan yaki da cutar ta COVID-19.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,655 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!