Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje, ya raka Sanata Shekarau gida cikin tawagar gwamnati

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya raka tsohon Gwamnan Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau gida cikin tawagar gwamnati bayan gudanar da Janaizar Marigayi Sani Dahiru Yakasai da safiyar Yau Jumma’a.

An dai binne marigayin ne a makabartar Tarauni da misalin karfe 10:05 na safe kamar yadda wakilin Freedom Radio a gidan gwamnati Abba Isah Muhammad ya ruwaito.

Wakilinmu namu ya kara da cewa, Gwamna Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau, sun shafe kusan rabin sa a suna ganawa a gidan Sanata Shekarau wanda ke Unguwar Mundubawa.

Sai dai Babu cikakken bayanin kan batutuwan da suka tattauna.

A baya-bayan nan dai alaka ta yi tsami tsakanin Sanatan da Gwamna Ganduje, lamarin da ya sanya gwamnan barin jam’iyyar APC.

To ko me ke shirin faruwa tsakanin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau?

Shiga shafinmu na Youtube da ke kasa domin ganin faifan bidiyon zuwan nasu gida.

https://youtu.be/aHdBYeOeGCQ

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!