Labarai
Ganduje ya sassauta dokar daukan mutum daya a baburin adaidaita sahu
Gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar da ta sanyawa ‘yan Adaidaita sahu ta daukar fasinja daya tilo bayan sake nazartar dokar, inda ta ce yanzu fasinjoji biyu za su rinka dauka amma ko wannensu da abin rufe hanci, don kare kai daga cutar Covid-19.
Shugaban hukumar kula da ababen hawa ta Jihar Kano KAROTOA Baffa Babba-Dan-Agundi ne sanar da hakan, inda ya ce matakin sassauta dokar ya biyo-bayan ganawa da kwamishinan sufuri na Jihar Kano Barista Muhammad Lawal da sauran masu ruwa da tsaki.
Zamu fara kama baburan Adaidaita sahu -KAROTA
Ya kara da cewa sauran masu motocin haya ma dokar ta shafe su inda aka rage muku yawan fasinjojin da suke dauka, sannan kuma wajibi ne su samar da sinadarin tsaftace hannu a cikin abin hawan na su.
Baffa Babba Dan-Agundi ya shaida cewa gamayyar tsaro da kungiyoyin masu motocin haya da na Adaidaita sahu ne za su yi aikin tabbatar da bin dokar, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.
Haka zalika ya gargadi jama’a wajen ganin sun mutunta dokar, domin ko duk wanda aka kama da laifin karya doka zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.
You must be logged in to post a comment Login