Coronavirus
Za mu kare dalibai daga Corona a lokacin rubuta jarrabawar WAEC – Dr, Bello
Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta yi shirin ko-ta-kwana ga daliban da ke shirin rubuta jarrabar kammala sakandire ta yammacin Afrika WAEC, don kare su daga kamuwa ko yada cutar Corona.
Babban Sakatare a hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano, Dakta Bello Shehu ne ya bayyana hakan a yau, ta cikin shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar freedom Rediyo, wanda ya mayar da hankali kan shirin fara jarrabawar WAEC ta bana.
A cewar sa, hukumar ta tsara daukan matakan ladabtarwa ga dukkanin makarantun da suka saba matakan kariya daga cutar corona don kuwa tuni gwamnati ta dauki matakan rarraba kayayyakin kariya a dukkanin makarantun don dakile yaduwar cutar.
Ya kara da cewa, annobar Corona ta dakatar da kudurin gwamnati na gyaran makarantu a jihar Kano, musammamma na samar musu da kujerun zama sai dai ya ce, da zarar komai ya daidaita za a fara gudanar da gyaran har ma da fara gudanar da kudirin nan na sanya almajirai a tsarin ilimin zamani.
Dakta Bello Shehu ya ce, an gano kalubale na rashin samar da fasahar koyo da koyarwa ta kafar internet, wanda gwamnati ta fara shirin samar da tsarin don bunkasa ilimi a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login