Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

NCDC : Yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai dubu 49068

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututka ta kasa NCDC ta sanar da karin samun sabbin mutane 298 da suka kamu da cutar COVID-19 a jiya Lahadi.

A sanarwar da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, yanzu haka adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya sun kai dubu arba’in da tara da sittin da takwas.

Haka kuma an sallami wasu mutanen dubu talatin da shida da dari hudu da casa’in da bakwai bayan tabbatar da cewa sun warke daga cutar.

Kawo yanzu dai cibiyar ta NCDC ta ce, mutane dari tara da saba’in da biyar ne suka mutu a sanadiyyar cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Cibiyar ta bayyana cewa jihohi 16 ne cikin tarayyar kasar nan aka samu karin masu dauke da cutar a jiya lahadi.

Anan jihar Kano kididdigar gwajin cutar a jiya Lahadi ya nuna cewa, mutum daya ne kawai ya kamu da cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!